25 Agusta 2021 - 10:11
​Najeriya Ta Amince Da Ingancin Alluran Riga Kifin Cutar Covit 19 Ta Sinopharm Ta Kasar Cana

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da alluran riga kafin cutar Covid 19 ta Sinopharm na kasar Cana, kuma zata karbi alluran na Cana har miliyon7.7 daga shirin nan na hukumar lafiya ta duniya wanda ake kira COVAX.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran neuters ya nakalto Dr. Faisal Shuaib, shugaban shirin samar da kiwon lafiya ta farko na kasa yana fadar haka.

Yawan wadanda suke kamuwa da cutar ta Covid 19 dai suna karuwa tun watan Yulin da ya gabata a tarayyar Najeriya. Kuma ya zuwa yanzu mutane miliyon 2 ne kaidai aka yiwa alluran riga kafin cutar, wanda shi ne kimani kashi 1% na yawan mutanen kasar.

342/